Shugaban Najeriya ya yi alkawarin samar da biza ga 'yan Afirka

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Najeriya ta ce, za a fara bawa duk wasu matafiya 'yan kasashen Afirka takardar izinin shiga kasar wato biza idan sun iso kasar daga farkon shekarar 2020.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari, ne ya ce yin haka ya nuna kokarin kasar na samar da zirga-zirga ba tare da shamaki a tsakanin kasashen Afirka ba.

Sanarwar ta zo ne watanni biyar bayan da Najeriya ta sanya hannu a kan wata yarjejeniya da nufin bunkasa harkokin cinikayya ba tare da wata matsala ba a nahiyar Afirka.

To sai dai kuma masu sukar shugaba Buhari, na zarginsa da kawo matsala a wajen hada kan kasashen Afirka.

Saboda ya sa an rufe dukkan iyakokin kasar tun a watan Augustan da ta wuce, lamarin da ya janyo matsala ta fuskar cinikayya a tsakanin kasar da sauran kasashe makwabtanta.

Shugaba Buhari dai ya yi buris da matsin lambar da ake masa a kan ya bude iyakokin kasar, inda ya ce an yi hakan ne domin kawo karshen shigo da abincin da ake yi ba bisa ka'ida ba.

An rufe iyakokin kasar duk da cewa Najeriya na daga cikin kasashen mambobin kungiyar ECOWAS.

Shugaban Najeriyar, bai bayyana randa za a bude iyakokin ba a lokacin da ya ke sanar da batun za a rika yi wa matafiya 'yan kasashen Afirka biza idan sun shigo kasar.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Ana dai yi wa Najeriya kallon wata babbar kasa a Afirka, wadda ke da manyan abubuwan da suka shafi tattalin arziki da kuma yawan jama'a.

To kowanne canji za a samu?

A yanzu, 'yan kasashen Afirkan da suke son shigo wa Najeriya, sai sun nemi takardar izinin shiga wato biza a kasarsu, to amma daga sabuwar shekara, abin zai sauya inda dukkan 'yan kasar Afirka da ke son zuwa Najeriya za su iya shiga jirgi su zo kasar, in ya so a filin jirgin saman sai su nemi bizar.

Wani bincike da bankin raya kasashen Afirka ADB ya fitar, ya nuna cewa 'yan kasashen Afirka na bukatar biza ne a kasashe 49 cikin 100, amma kuma suna samun bizar ne a kasashe 26 cikin 100 idan sun sauka a can.

Wannan layi ne

A cikin kasashen Afirka 54, kasashen da suka bayar da dama ta samun takardar shiga kasarsu wato biza idan an shiga cikin kasar, su ne Benin da Senegal da Seychelles da Rwanda da kuma Ghana.

Kasashen da ake shan fama kafin a samu bizarsu a 2019 su ne, Equatorial Guine da Libya da Sudan da Eritrea da kuma Sudan ta Kudu.

Kasar Habasha ita ce aka bayyana da kasar da ta fi kowacce koma baya ta bangaren samun biza, to amma tun lokacin da ta sanar da manufar samar da biza ga 'yan kasashen Afirka idan an shigo kasar, sai aka samu ci gaba sosai.

An dai sanya Najeriya a matsayin kasa ta talatin a cikin jerin kasashen Afirka da ake wuyar samun visa a 2018.

Kasar Kenya, wadda ita tafi sauran kasashen Afirka yawan tattalin arzik a Gabashin Afirka, a sanyata a matsayin kasa ta goma sha uku inda ta dawo baya a shekarar 2018.

Kungiyar kasashen Afirka dai na ta kokarin ganin an samar da fasfo guda ga dukkan 'yan kasashen Afirka, ta yadda tafiye-tafiye a cikin nahiyar za ta yi sauki ba sai an bukaci biza ba.

A shekarar 2018, mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya yi korafin cewa sai da ya nemi bizar kasashe 38 kafin ya yi tafiye-tafiye a cikin nahiyar Afirka.

Iyakar Rwanda da Uganda
Bayanan hoto, Iyakar Rwanda da Uganda da aka rufe kusan shekara guda

A wajen taron da kungiyar kasashen Afirka ta yi a 2013, an cimma matsayar cewa za a rika ba da damar samun visa cikin sauki ga dukkan 'yan kasashen Afirka a 2018.

Sai dai kuma ga dukkan alamu ba a cimma hakan ba a wasu kasashen Afirkan.

Kamar Misali, Afirka ta Kudu a yanzu tana shirin kirkirar wata hukuma a 2020, da za ta rika sanya ido a kuma kawar da bakin haure wadanda ba su da cikakkun takardu.

Sannna, an rufe iyakar Rwanda da Uganda tun a watan Maris din 2019, bayan da shugaban Rwanda Paul Kagame, ya zargi takwaransa na Uganda Yoweri Museveni, da kokarin bata masa gwamnati.

Mr Museveni, dai ya musanta wannan zargi, kuma duk wani yunkuri da ya yi na ganin an bude iyakar ya ci tura, kamar yadda kiraye-kirayen bude iyakokin Najeriya ma ya ci tura.