Dalilai takwas da ka iya hana mace ganin al'adarta

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, BBC 100 Women
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari,
Ana kiran ɓatar watan haila ko rashin samun al'ada ga mata masu shekaru na haihuwa da 'amenorrhea', duk da cewa ciki shi ne mafi shahara daga cikin dalilan da ke haddasa hakan, masana sun ce akwai wasu dalilai da dama da ka iya janyo tsaiko ko dakatar da zuwan jinin haila.
A mafi lokuta, mata masu haihuwa kan sami al'ada duk bayan kwanaki 28. Amma hakan na iya sauyawa ya zama kamar tsakanin kwanaki 24 zuwa 35, kuma hakan ba abu ne na damuwa ba.
Idan al'ada ta ɗauke na ɗan wani lokaci, hakan ba matsala ba ce sosai, amma kuma idan ta dingi ɗaukewa a lokaci-lokaci, hakan ka iya zama alamar wata matsalar lafiya da ke buƙatar kulawa.
"Ya kamata mace ta san jikinta da yadda yake aiki domin fahimtar lokacin da wani abu bai yi daidai ba, ko wata matsala" in ji likitar mata, Dr. Amira Alkourdin Martinez, a wata hira da ta yi da BBC.
"Kowane jikin mace daban yake aiki; babu mata biyu da yanayi iri ɗaya."
Hukumar lafiya ta ƙasa ta Birtaniya (NHS) ta shawarci mata da su nemi ganin likita idan suka daina samun al'ada na tsawon wata uku a jere ba idan har ba ciki bane, ko kuma idan al'adar ta daina zuwa kafin mace ta kai shekara 45.
A Amurka kuwa, asibitin Mayo Clinic ya ba da shawarar a kai yarinya asibiti idan ta kai shekara 15 kuma bata fara samun al'ada ba.
A cewar waɗannan cibiyoyin biyu, bayan ciki, akwai dalilai guda takwas da aka fi sani da za su iya haddasa amenorrhea wato ɓatar wata.
1. Gajiya ko wahala
Gajiya ko wahala na ɗaya daga cikin babbar dalili da ke saka mace ta sami ɓatar wata ko hana mace samun al'ada a zamaninmu na yau in ji Dr Amira Alkourdin Martinez.
Lokacin da mutum ke ɗauke da gajiya ko cikin wahala, jiki na fitar da wasu sinadaran hormones kamar adrenaline. Waɗannan sinadaran na taimakawa jiki ya shirya kare kansa idan akwai wani haɗari.
Idan gajiya ta ɗauki dogon lokaci, tana iya shafar yadda mace ke samun al'ada. Zai iya sa kwanakin al'adar ta yi tsawo ko ta yi guntu ko kuma ma ta daina zuwa gaba ɗaya, ko kuma ta zama mai zafi sosai.
A wasu lokuta, gajiya na iya sa mace ta samu al'ada sau biyu a cikin wata guda.
Idan gajiya ce ta janyo jinkirin al'ada ko hana ta zuwa, hukumar lafiya ta ƙasar Birtaniya (NHS) ta ba da shawarar yawan motsa jiki akai-akai ko koyon dabarun numfashi domin samun natsuwa.
Idan wadannan basu yi tasiri ba, ana iya ganawa da ƙwararren likita ko mai ba da shawara kan damuwa da gajiya domin rage yawan samun gajiya da fargaba.
2. Mummunar rama
Cin abinci kaɗan sosai na iya hana jiki fitar da sinadaran hormones da ake buƙata domin haihuwa (wato fitar kwai daga mahaifa).
Ƙwararren masanin abinci na iya taimakawa mutanen da suka rame sosai – musamman waɗanda adadin nauyinsu (BMI) ya sauka ƙasa da 18.5 – su ƙara ƙiba ta hanyar da ba ta cutar da lafiya ba.
Idan rama sosai ta faru sakamakon wata matsala irin ta rashin cin abinci kamar anorexia, to a mafi yawan lokuta, sai an nemi taimakon likitan kwakwalwa

Asalin hoton, Getty Images
3. Ƙibar da ta wuce kima
Yawan kiba na iya sa jiki ya riƙa fitar da sinadarin oestrogen fiye da kima, wanda shi ne ɗaya daga cikin hormones da ke kula da tsarin haihuwar mace.
Idan wannan hormone ya yi yawa, zai iya kawo sauyi a yadda mace ke samun al'ada, kuma a wasu lokuta ya sa al'adar ta daina zuwa gaba ɗaya.
Ga mata masu fama da amenorrhoea (rashin zuwan al'ada) kuma suke da kiba ko nauyinsu yayi sama da 30, likitoci kan tura su ga masanin abinci domin su taimaka musu su rage kiba cikin lafiya.
4. Tsananta motsa jiki
Wahalar da ke tattare da motsa jiki mai tsanani na iya shafar hormones da ke kula da al'ada, kuma rasa kitsen jiki da yawa na iya hana fitar ƙwai.
Ga ƙwararrun 'yan wasa, masana lafiyar wasanni na iya ba da shawara kan yadda za su ci gaba da yin atisaye ba tare da ya cutar da lafiyarsu ba.

Asalin hoton, Getty Images
5. Yanayin da ke shafar jakar ƙwayaye na mata (PCOS)
'Polycystic ovaries' yanayi ne na mata da ke shafar jakar ƙwayayen mata.
Waɗannan ƙwayoyin yawanci ba sa iya fitar da kwai, don haka fitar kwai ba ya faruwa.
A cewar hukumar lafiya ta NHS a Birtaniya, wannan yanayi na shafar mace ɗaya cikin mata goma. Kuma ita ce ke da alhakin ɓatar wata a kusan kashi 33 cikin 100 na lokuta.

6. Shekarun ɗaukewar jinin haila
Bayan ɗaukar ciki da kuma shayarwa, ɗaukewar jinin al'ada gaba ɗaya wato menopause na daga cikin dalilan da ke hana mace samun al'ada.
Yayin da mace ke kusantar menopause, sinadarin oestrogen na raguwa a jikinta, kuma fitar kwai na raguwa ko daina zuwa akai-akai.
ɗaukewar al'ada gaba ɗaya yawanci na faruwa ne tsakanin shekara 45 zuwa 55.
Amma binciken likitoci ya nuna cewa mace 1 cikin 100 na fuskantar ɗaukewar al'ada gaba ɗaya tun kafin shekara 40. Wannan ana kiransa 'premature menopause'.
7. Magungunan hana haihuwa
Wasu magungunan hana ɗaukar ciki kamar kwayoyi da allura, da waɗanda ake dasa wa cikin fata na iya hana mace samun al'ada (amenorrhoea).
Ko bayan mace ta daina amfani da kwayar hana ɗaukar ciki, zai iya ɗaukar lokaci kafin jikinta ya fara fitar da ƙwai yadda ya kamata.
8. Sauran cututtuka da magunguna na dogon lokaci.
Ɓatar watan al'ada na iya faruwa sakamakon wasu cututtuka na dogon lokaci kamar su ciwon suga ko matsalolin hormones kamar hyperthyroidism.
A cewar asibitin Mayo Clinic da ke Amurka, wasu magunguna ma na iya hana mace samun al'ada, kamar su magungunan taɓin hankali, da magungunan ciwon daji da magungunan damuwa, da magungunan hawan jini da na abin da jiki baya so.