Lafiya Zinariya: Hatsarin haihuwa a gida ga mai ciki

Bayanan sauti
Lafiya Zinariya: Hatsarin haihuwa a gida ga mai ciki

Babban hatsarin haihuwa a gida ga mace mai juna biyu shi ne rasa ranta saboda wasu matsalolin da suka haɗa da doguwar naƙuda da zuban jini, a cewar likitoci.

Rashin ƙwararriyar mai karɓar haihuwa da bata san muhimman matakan da ya kamata a ɗauka ba, idan aka samu matsala a wajen haihuwa na taimakawa wajen rasa rayukan matan da ke haihuwa a gida.

Hakan na cikin manyan dalilian da suka sa yawan mace-macen mata masu ciki ya ƙaru a Najeriya zuwa 1047 a cikin kowace haihuwa 100,000, a shekarar 2020.

Wata maƙala da hukumar lafiya ta duniya reshen Afrika ta wallafa a watan Maris, 2023 ta bayyana cewa, a shekarar 2020 an samu mutuwar masu juna biyu 531 a cikin kowace haihuwa 100,000 a nahiyar.

Afrika ce ta samu kashi 69 cikin dari na mace-macen mata masu juna biyun da aka samu a duniya a shekarar 2020.

A wannan shekarar ƙasar da ta fi kowacce fuskantar yawaitar mace-macen masu ciki a Afrika ita ce Sudan ta Kudu, sai Chadi sai ta ukunsu Najeriya.